Sabuwar Fassarar India Sultan Film Factory
Sai kokarin bace musu suke, amma abin y ci tura, duk lokacin da suka boye masu na wani lokaci, cen sais u gan su, a haka har safiya taw aye rana ta haur tsakiya si gudu suke, su kuwa ko alamun gajiya babu a tattare da su sai biyar su suke yi. Cen tsoho ya fadi ya kas tashi, suk tsya domin su bashi dauki, amma ya umarce su da su tafi kawai su bar shi, da kyar hadi da kukansu suka aminta suka bar shi, kasancewar ya nuna musu shi ba wata attaka da zai iya tabukawa, idan kum suka tsay, suma rayukansu za sui ya karewa, da ayi haihuwar guzuma, gar shi su barshin, ko ba komai zai rage masu saurinsu. Kan haka suka barshi suk ci gaba da gudun nemn kubuta daga mutuwa, tun basuyi nis ba, suka jiwo kararsa, almun sun farmsa ne, ko da suka waigo suk gay add suke cin namansa danye, tausayi ya hana sui ya kallon wannan rashin imani na wadannan mutanen, ko mu ce halittun. Suka ci gaba da gudu, ba treda sanin ina za su nufa ba.
Suna cikin gudu har suka zo wurin wani dutse mai kogo a jikinsa, ba tareda tsaiko ba suka runtuma ciki, haka suka cig ba da gudu a cikinsa, duk da kogo ne, a ciki ynada girma da fadi sosai, kamr dai wata katuwar hanya, ba abinda suke haduwa da shi idan ba kashin manyan dabbobi ba, gawarwakin manyan tsuntsaye, sunfi gudun awa biyu kafin su fita daga wannan kogon, da suka fita, kuma ba su tsaya ba a haka suka ci gaba da gudu, har sai da suka tabbatar da wadannan mutanen sun daina biyarsu, sai suka tsaya, suka rasa me ke damuwarsu, dattin jikinsu ko yunwar cikinsu ko gajiya da suka kwaso ta wannan gudun ceton rai.
A bangaren halittun kuwa, da suka g sun nema basu gan su ba, dole suka hakura suka koma mazauninsu.
Related Post
“kai lallai mun kuru, wadannan marasa imanin da sun sami kama mu ai da tuni mun zama gawa, ji fa yadda suke tazgar naman dattijo, lallai duk wanda ya tashi a jeji dole ya yi dabi’u irin na dabbobi” Fate ta fada cikin muryar shessheka, Abdulsamad kuwa sai harararta yake yi a ransa yana cewa, kanku ake ji, ni yunwar cikina ita t dame ni.
“ba shakka ubangiji ne ke nuna buwayarsa garemu, yana kuma so mu kara gode masa da sanin cewa shi kadai zai iya kubutar da mu daga wannan ala’in, sau da yawa ubangiji yakan yi abu domin y jarraba imanin bayi, mu tamu jarabawa ke nan, sai mu dage mu cit a sosai, duk da haka, Fate ki kara tunani kan hujjoji d abubuwa da ke gudana, kisn cewa musulunci ne kadi addinin gaskiya, ki sallama, bakisani ba ko nan ne karshen rayuwarki” Ameer ya fada.
“har yanzu in bukatar hujjoji da za su gamsar da ni fiye da wadanda na mallaka.
Aseeya ta karbe, “ai kuwa ki tsaya wurin jiran hujjoji har lokaci ya kure maki, kinga gwanda ke, ni bari inyi sallolin da ke kaina” ta fada dai dai lokacin da take kokarin gyaran wurin da za ta yi taimama.
Bayan sun kammala sallolinsu, Ameer ya gabata domin ya gabatr da kansa. Sunana Shaheed ni haifaffen garin Kangiwa ne a nan Kebbi state, amma an haife ni a garin Sokoto a a unguwar ‘Yar Marina, a nan na far girma, si dag baya muka dawo nan Kebbi, nan nayi karatuna gaba daya, bancin university inda na karanci Pharmcy a UDUS. Ni kadai ne a wurin mahaifina da mahaifiyata, hakn ta san a taso cikin kulawa, duk abinda nake so ina samu dag mahaifiyata musammn, ia wani rubutu ne da ya shafi, boarder ta garin Dole kaina, shi ne dalilina n zuwa Kamba.
“taff! Yanzu kan rubutu shi ne za ka taso tun daga uwa duniya? Ai da sai ka rubuta duk abinda y zo maka a kai, naga galibi mrubuta hake kuke yi, ya fi maka wahalar bata lokaci da kashin kudin mota”
“hmmm! Abokina kenan, shi rubutu, daga cikin abubuwan da ke inganta shi, akwai kwakkwaran bincike, ba haka kawai ake rubuta duk abinda ya zo wa mutum ba, hakan ke sa marubuci ya fuskanci zagi da makamancinshi a wurin makaranta, yanada kyau, duk abinda za ka yi rubutu a kai, ka tabbatar haka abin yake, idan ma a kirkirarren labari ne, wurare da kayi amfani da su ko garuruwa, ka tabbatar yadda ka rubuta hak abin yake, duk da kai marubuci kanada damar kirkirar gari ka sk ms suna da kanka, amma idan ka yi amfani da gari sannne, dole ka rubutashi yadda yake. na fahimta” Abdul ya fada.
Poster
Suka ci gaba da tafiya har suka tarar da wata ‘yar bukka a tsakiyar Jeji, cikin fari ciki, suka leka bukkar, amma ba kowa a ciki, kuma ba alamar mutum na zama a ciki, hakan yasa suka ci gab da tafiya, yunwar cikinsu kadaai tai she su. Sai faman jn kafafuwansu suke, shi Abdul a bangrensa kawai ayi shu, domin har hawaye ya zubar kan yunwa, Fate kuwa sai faman hasaso hujjiji take daga zuciyarta tana kwatantawa da addininta.